Abubuwa guda uku da zaku iya yi da kuma baza ku iya ba a lokacin al’adar ku

Lokacin nan na wata ya kai kuma

Al’ada. Suna zuwa kuma suna tafiya, ko ba haka ba? Amma wasu lokuta idan suka zo, baku sanin abun yi. Sai abubuwa su rikitar daku.

Duk da haka, al’ada na iya yin sauki idan kuka san abun yi. Ga dabaru guda uku da zasu shirya ku.

Kada kuyi: Kada ku ci abinci masu mai, gishiri, da kuma kayan zaki
Zasu saka ku kumbura, gajiya, kuma su canza halayyar ku. Kuma zasu saka nonuwar ku taushi sosai. Abu daya kuma daya kamata ku kauce shine abubuwa dake da madara. Eh, madara na cike da alli da kuma sinadaran abinci. Amma bai da kyau muku a lokacin al’ada saboda yana kara iska da kuma ciwon ciki. Saboda haka yana da kyau ku guje madara har sai al’adar ku ya kare. Eh, mun san cewa kauce wadannan abubuwa babu sauki– musamman idan kuna son su. Amma zaku iya yi.

Kuyi: Kuci kifi, ganye da kuma ‘ya ‘yan itatuwa
Zasu kara gyara halayyar ku kuma inganta lafiyar jikin ku. Ku sha kofin shayin citta da zuma mai zafi. Yana taimaka rage ciwon cikin. Idan kuna zub da jini sosai, ku ci abinci dake da ma’adanin kimiyya dake kara karfi kamar wake, kwai, ganyen ugu da kuma danyen agade domin ya rage hatsarin rashin lafiya dake sa kwayoyin jini suyi karanci a jikin mutum. Kuma, ku sha ruwa sosai.

Kada kuyi: Kada ku saka fararen kaya
Idan kun saba datti da kayan ku a lokacin al’adar ku, ku guje saka fararen kaya. A ta nan, baku bukatan duba bayan ku a kowane minti. Kuna cancancin kwanciyar hankali a lokacin al’adar ku.

Kuyi: Ku saka bakaken kaya
Zasu fi kwantar muku da hankali kuma ya kara tabbacin ku. Kuma, idan kuka yi datti da kayan ku, ba wanda zai lura. Sai ku lallaba ku je ku canza kayan ku idan kuna bukata.

Kada kuyi: Kada ku tsallake yin wasannin motsa jiki
Koda gadon ku na rudin ku, kada ku kwanta a wajan kawai. Akwai wasannin motsa jiki masu sauki da zasu iya sassauta ku. Shine ya mu kawo zuwa…..

Abun da zaku yi: Wasannin motsa jiki kamar mika jiki da kuma yin tafiya
Suna rage tashin hankali, gajiya da kuma ciwon ciki. Zasu taimake jikin ku. Ku tashi yan mata, ku fara aiki.

Ku tuna, baku kare kanku daga daukan ciki da kuma kama cutar jima’i ba koda kuna al’ada. Kuna da wani tambaya? Kuyi wa wata amintaccen babban mutum kamar yar uwar ku, ko Innar ku ko kuwa wata kwararriyar likita magana.

Menene abubuwan da kuke yi da kuma abubuwa da baku yi a lokacin al’adar ku. Gaya mana dukka a wajan sharhi.

Share your feedback