Karanta wannan makalar saboda ki fahimci bakon ki na wata wata da kyau!
Muna son muyi miki magana akan lamari babba na ‘yar mace. A-L’-A-D-A.
Jinin haila! Wannan abun dake faruwa da kowane ‘yar mace a gaba dayar duniya.
Abun tsoro akan yin al’ada shine rashin sanin abun dake faruwa.
Jikin mu ne, alhakin mu ne mu san yadda yake aiki.
Bari mu amsa wasu matsalolin ku.
Nkiru daga jihar Enugu: “shekaru na goma sha biyar! Kuma ban fara al’ada ba tukunna. Duka abokai na namun dariya, suna cewa ni karamar yarinya ce. Akwai abun dake damu na ne?
Kina da lafiya! Kada ki damu.
Yawancin yara mata na fara jinin haila tsakanin shekaru goma sha biyu da goma sha uku. Wasu mata na farawa da lati. Daga shekaru goma sha shida.
Ki tambaye mahaifiyar ki shekerun ta nawa sanda ta ga al’adar ta na farko. Irin wadannan abubuwan zasu iya zama abun da kika gada daga iyayen ki.
Kuma dai, yan mata dake wasannin motsa jiki ko kuma wanda suke da siririn jiki sosai na samun jinkiri a jinin hailar su.
Zeriya daga jihar Kano: “shekaru na goma sha takwas kuma na lura cewa al’ada na baya faruwa koda yaushe. Amma jinin dake zuba a lokacin al’ada ta na banbantawa. Wasu mata na zub da jini sosai fiye da sauran mata."
Ga wasu sannanen sanadin dalilin rashin samun al’ada koda yaushe:
Kada kiji tsoron samun amsa. Idan kina damuwa, ki tambaye mahaifiyar ki. Idan bata iya shawo kan matsalar ba, ki tamabye wani likita. Idan suma basu iya ba, ki sake tambayar wani likita. Jikin ki ne, rayuwar ki ne, kuma ra’ayin ki ne. ki gaya mana damuwan ki a shafin sharhin mu.
Share your feedback