Na aske gashin ko kada na aske?

Koda menene shawarar da kika yanke, abun muhimmancin shine tsaftar jikin ki dana muhalli

kin lura gashin dake karkashin hamatan ki ko na fargin ki?

Toh rashin lura da gashin dake wajan nan zai iya jawo miki kamuwar cuta ko warin jiki.

ki tabbata kinyi wanka so biyu a rana kuma ki wanke wajajen nan da kyau da sabulu da ruwa, sai ki shafa masa hoda ko tularen jki saboda zai taimaka kashe zufa da wari.

Wata hanyar lura da gashin nan shine yin aski.

koda yake yankin shawarar yin askin na wajan ki, ga wasu abubuwa da ya kamata ki sani.

Yadda za kiyi aski
Ki jike wajan kafan ki aske. yin aski idan wajan ya bushe zai iya jawo miki ciwo kuma yana da radadi. yin aski a bushashen waje zai iya jawo miki marurai.
lokacin daya kamata ayi aski shine lokacin wanka.

Lokacin daya dace ayi aski
Babu wani lokaci da aka yi seti na yin aski. Kiyi aski lokacin da kika ga kamar gashin yayi girma da yawa.
Zaki iya wa wani babba da kika yarda da akan lokacin daya dace kiyi aski. ki tambaye su ko kin shirya fara yin aski. Idan kin kai, zasu iya koya miki yadda zaki yi aski.

Abun da zaki amfani kiyi askin
Kiyi amfani da sandan aski ko da reza.
Kada kiyi amfani da wuka, ko wani dakusashen ko sandan aski mai tsatsa.
Zaki iya tambayar wani babba da kika yarda da ya taimake ki samun reza ko sandan aski mai kyau.

Bayan kinyi askin
ki shafa mai a wajan.
vaseline da mai kade na da kyau ma wannan.
Ki guje mai dake da kamshin kamar fure. Ma’adanin kimiyya dake cikin yawancin mai zai iya sanadin rauni na jiki kuma ya jawo kamuwa da cuta.

Kada kiyi amfani da sandan aski ko reza tare da wani. Zasu iya jawo miki kamuwa da cuta.

A ringa ajiye sandan aski da aka yi amfani da a wajan daya bushe saboda idan kina son ki kara amfani dashi. Wannan domin a guje tsatsa ne.

Yankin shawarar mu ne mu aske gashin mu koda yaushe. Koda menene muka yanke shawarar cewa shine mafi tsira yana da muhimmanci.

Kina da wasu tambayoyi akan ajiye gashin ki ko askewa?

Kiyi mana magana a sashin sharhin mu.

Share your feedback