Meke faruwa a cikin ciki na?

Ganarwa mai sauki da zaki fahimci akan al’ada

Kin taba al’ajabin abun dake faruwa a cikin ki kafin ko bayan al’adar ki?

Ga Tafiyar.
Tafiyar na farawa daga wajan dake samar da kwai a jikin ki. Suna ajiye duka kwan da zaki samu a gaba dayar rayuwar ki.

Kowanda mace nada wajan samar da kwai a jikin ta guda biyu. Kowanda wata, kwai daya zai yi tafiya daga wajan nan da ake samar da kwan zuwa bututun ciki.
Daga bututun cikin, kwan mu zai koma mahaifa.

Mahaifan mu zai sa bangon sa ya kara kauri. Yana kirkira matashi domin kwan ya boye idan wannan kwan ya hadu da maniyyi suka halitta jariri.

Maniyyi na zuwa daga maza. Yana daukan maniyyin tare da kawan ya halitta jariri.

Idan kwan bai nuna ba a cikin sati daya ko biyu, jikin mu zai yanke Shawara yace shikenan.

Mahaifar ki na tura duk abunda baya bukata, harda dogon zanen nan na cikin ciki da kuma kwan. Wannan yana sakamakon zuwa abun da ake kira al’ada.

Wannan hanyoyin tafiyar na faruwa kowane wata a cikin kusan duka baligin rayuwar mu.

Yanzu da kika san abun dake faruwa a cikin ki. Ba abun mamaki bane dalilin dayasa yana miki zafi wasu lokuta. Jikin mu nada hazaka da bada mamaki, ko ba haka ba?

Gaya mana akan masaniyar al’adar ki ko damuwar ki a shafin sharhin.

Share your feedback