Dalilin da yasa cewa “A’a” shine abun da ya “dace”

ki kare kanki kuma ki kare rayuwar ki na gaba

Wasu lokuta abun da yafi tsira sWine cewa a’a da zarra, ba tare da tsoro ba. kamar Ngozi.

Emeka nason ta zama budurwar sa. Shekarun sa ishirin da daya, ita kuma goma sha biyar.
Ngozi da Emeka na abokantaka da dadewa. Wasu ranaku zata zauna da makwafcin ta suyi labari da shi.

Kan lokaci suke kara shakuwa sai ya tambaye ta ta zama budurwar sa.

Sai taki.

Emeka yaki ya fidda rai.

Ta gaya masa tana son ta maida hankali akan horaswar ta a gidan biredi. Tana kotan yin cake kuma tana son ta fara siyar dasu bada da jimawa ba. Ta gaya masa zai dauki hankalin ta.

Wannan bai hana shi yin tashi ba. Sa ta fara gujen sa.

Ta gaya wa abokan ta Amara da Joy akan sa.

Suka gaya mata cewa kyakkyawan namiji ne.

Wai yana da kudi kuma yana yawan siyo musu lemun kwalba. Sun gaya mata ta yarda masa.

Sun gaya mata kowa nada saurayi kuma tana yi kamar tsohuwa.

Wani maraice Emeka yazo gidan su Ngozi. Ya lura cewa ba kowa a gidan.

Sai ya fara yabon ta. Ta gaya masa ya tafi nan take tunda ba kowa a gidan.

Ya ki sai yaso ya taba ta. Ta tura shi.

Ya gaya mata ta bashi dama.

Ya gaya mata kowa na kwada yin jima’i kuma tana yi kamar karamar yarinya. Ya ma alkawari wai zai kashe mata kudi.

Ta gaya masa A’a sai ta roke shi ya tafi. Ta fara ihu bayan yaki tafiya. Emaka ya ji tsoro ya tafi.

Da mahaifiyar Ngozi ta dawo da yanma sai ta gaya mata abun da ya faru.

Mahaifiyar ta tayi mata tafi da bata ajiye abun da ya faru sirri ba. Ta gaya wa Ngozi cewa tayi abun da ya kamata da ta gaya wa Emeka A’a. Ta gaya mata kada abun da ya faru ya bata tunanin cewa dukka maza basa da hali mai kyau.

A bisa mahaifiyar Ngozi wata rana idan ta shirya yin soyayya zata hadu da wani saurayi mai hankali.

Akwai wanda yake sa ki yin abun da baki son yi? Kice a’a, kamar Ngozi.

Kina ganin Ngozi tayi abun da ya dace? ki gaya mana a sashin sharhin mu.

Share your feedback