ZAN TABA KARA TSAYI?

Yadda na bi da fargaban karin girma

Na tsana duk lokacin da malamar makaranatar mu tace mu “muyi layi bisa ga tsawon mu” . Nice gajeriyar ajin mu. Dole kowane lokaci na tsaya a gaba. Shekaru na goma sha biyar, amma yan ajin mu sun ce ina kama da mai shekaru goma. Abokiya ta Ola ta fara saka rigar mama a shekaru goma sha uku. Ni kam ina saka wata karamar riga kafan na sanya kayan makaranta na. Duk da haka banda babban nonuwa.

Wata rana na gaya wa mahaifiya ta ina tunanin wani abu na damu na. Na roke ta ta kai ni asibiti saboda bana girma kamar sauran mutane. Ta kai ni wajan Mrs Eze, Mashawarcin na a makaranta. Da farko, Ina ta haushi. Amma bayan da muka gama magana, ina murna. Tayi mun bayani komai sosai.

Mrs Eze ta mun bayani akan komai na balaga. Lokaci ya kai da jikin ki zai fara bunkasa zuwa mace. Akwai alama daban daban. Yarinya zata fara kara tsawo, gashi zai fito mata a karkashin hamata, kurajen al’ada zai fara fitowa, duwaiwan ta zai kara girma, nonuwan ta zai fara girma kuma zata fara jinin haila. Wasu mata na farawa da sauri a shekaru bakwai, amma wasu basu farawa sai a shekaru goma sha uku. Wasu mutane kuma sai a shekaru goma sha biyar ko goma sha shida, basu samun ko daya daga cikin wadannan abubuwan. Baya nufi cewa akwai abun dake damun su. Kowane mace na nan daban. Suma zasu yi girma.Amma mai yiwuwa nasu yayi lati fiye dana abokan su.

Ga wasu abubuwa da zasu iya shafi yadda zamu yi girma:

  • Idan iyayen mu basu da tsawo, mai yiwuwa baza muyi tsawo ba. Idan iyayen mu basu yi girma ba da sauri, zai iya faruwa da mu.
  • Mai yiwuwa bamu cin abinci da kyau. Abinci kamar wake, kwai, ‘ya ‘yan itatuwa da ganye zasu taimake mu girma da karfi.
  • Kin sani cewa, saboda muna kan girma muna bukatan karin bacci? Ya kamata muna baccin awa takwas kowane dare.

Idan kin kai shekaru goma sha takwas kuma baki ga al’adar ki ba ko sauran alamar balaga, kije kiga likita. Kawai domin ki duba ko kina da wani matsala.

Jikin ki na canzawa da sauri ko da hankali fiye dana abokan ki? Gaya mana a shafin sharhin mu.

Share your feedback