Uwaye ma zasu iya zama gagarumai
Wasu lokuta muna tunanin mahaifan mu sunyi tsufa su fahimce damuwar mu na matashi.
Gaskiyar shine mahaifan ku ma budurwai ne a wani lokaci.
Sun taba sha’awar yan maza.
Sun taba masaniyar canje-canjen jiki da kuke masaniya yanzu.
Mai yiwuwa sun tambaya wadannan tambayoyin da kuke tambaya yanzu.
Tambayoyi kamar
– Meyasa ban ga al’ada na ba?
– Meyasa abokai na suka fi ni tsayi?
– Meyasa nonuwa na basu girma?
– Ya zan gaya wa wani yaro da nake so cewa ina sha’awar sa?
Sunyi masaniyar dukkan wannan.
Akwai abubuwa da yawa da zamu iya koya daga mahaifan mu.
Kuna tsoron yi wa mahaifan ku magana? Ga dabaru da zasu taimake ku
Ku naima wani abu da mahaifan ku ke son yi
Yin girki ne, ko rawa, ko kuwa wasan motsa jiki? Kuyi ta da ita. A wannan hanyar zaku iya kara gina dangantakar ku da ita.
Ku koya yin magana
Ku koya yadda zaku riga fadin abun dake zuciyar ku. Kada ku boye su. Ku fara gaya mata yan kananan abubuwa kamar yadda kuka kwashe lokaci da abokan ku, ko wani sabon abunda kuka koya. Wannan zai taimaka gina amincewa da dangantakar ku idan kuna son ku tatauna abubuwa masu muhimmanci.
Tunanin ku ya zama mai kyau
Kada ku tunanin ko mahaifan ku zasu muku ihu. Kuyi tunanin zasu fahimce ku, kuma zasu so su muku magana. Yin tunani haka zai kara karfafa ku kuyi magana dasu.
Ku kasance masu aminta
Kuna cikka alkawarin ku koda yaushe? Cikka alkawarin mu (da kuma bayar da bayani idan muka kasa) daya ne daga cikin hanyar da zamu gina da kuma kula da amintar mu. Idan manya suka san cewa zasu iya yarda da mu, zai yi musu sauki su saurare mu da kuma amsa mu idan muka same su.
Ba lallai sai mahaifan ku kawai zaku iya yin wa magana ba.
Zaku iya yin wa yan uwan mahaifan ku, yayin ku ko kuwa wani amintaccen babba kusa daku.
Mahaifan ku nada saukin yin magana da? Kuna son mahaifan ku su kara fahimce ku? Kuyi mana magana a sashin sharhi.
Share your feedback