Kin Fara Al' Ada?

Ga Wasu Bayanai:

Tunanin ku (8)

Ko wane wata bututun mahaifa na sakin ƙwai, kuma shimfiɗar mahaifarki (mahaifa) tana daɗa kauri domin shiryawa ko kwan zai sami haɗuwa da maniyyi (wato lokacin da ki ka sami ciki). Idan ƙwan bai sami haɗuwa da maniyyi ba a wannan watan, wannan shimfiɗar mai kauri sai ta fashe kuma ta fito cikin wasu kwanaki kaɗan – wannan ita ce lokacin al’adarki. Da zaran kin fara al’ada jikinki zai iya ɗaukar ciki kuma ki sami yaro idan ki ka yi jima’i. Dole ki tabbatar kin kare kanki daga ɗaukar ciki idan ba ki shirya samun jariri ba. Abin da aka saba ne ki sami ciwon ciki kaɗan lokacin al’ada. Zai taimaka idan ki ka saka jakar ruwan ɗumi a cikinki. Yana da kyau ki motsa jiki kaɗan kamar tafiya maimakon ki zauna a wuri guda. Idan ciwon yayi yawa, ki tuntuɓi likita. Idan ba’a samun audugar mata kuma ki na amfani da tsumma, ki tabbata cewa tsumman yana da laushi, wankakke kuma wanda ya bushe sosai. Idan ba ki yi al’ada ba, jikinki yana aika miki da saƙo ne, sabo da haka ki lura. Yi ƙoƙarin in abinci mai lafiya kuma ki samu isasshen bacci. Idan ba ki yi al’ada ba a wasu watanni kaɗan, ya kamata ki je ki ga nas ko likita

Share your feedback

Tunanin ku

wannan dai dai ne

March 20, 2022, 8:04 p.m.

Kuna godiya da wannan bayani.

March 20, 2022, 8:04 p.m.

Shin mace mai ciki tana al Ada ne

March 20, 2022, 8:04 p.m.

Latest Reply

Hey Hawwy!

Toh taya zata ganeh idan yana zuwa

March 20, 2022, 8:04 p.m.

Latest Reply

Dole ne ai xaki gan shi idan yana xuwa

I Dan Mace Tana Da Ciki Kuma Sei Ta Sadu Mijinta Har Yakaye Ga Mijin Ya Kawo Maniyi In Maniyin Zai Zauna,

March 20, 2022, 8:01 p.m.

Kamar Da Yaushe Ne

March 20, 2022, 7:59 p.m.