Mene Ne Balaga?

Yanayin Canjin Jiki.

Tunanin ku (6)

Balaga wani lokaci ne da ke kawo canji-canje na wasu bangare a jikin ki kuma zaki samu canji a tunanin zuciyar ki. Ga wasu abubuwa da za ki iya tsammani:

Za ki ga nononki na kara girma da bulowar gasu a marar ki. Wannan ne lokacin da za ki fara al’ada kuma. Abu ne da baki saba gani ba ki ji kin fita daban kuma ke ma za ki dinga damuwa da canjin a jikinki. Nan da nan kinyi fushi kiji duk kin damu. Abu ne mai kyau ki yi magana da wani idan kin fara ganin wannan canjin a jikin ki. Balaga na faruwa ga ko wace yarinya ko yaro, amma ba duka a shekaru ko lokaci guda ba. Yanayin girman kiya banbanta da na kawayen ki. Wannan na iya sa miki damuwa ko kiyi tunani cewa an barki a baya – to amma ki tuna cewa kowa daban ya ke kuma jikinki na girma ne ta hanyarsa. A yayin balaga za ki fi son kiyi magana da ƙawayenki fiye da manyan mutane. Kiyi kokarin zaɓen ƙawayen kirki na arziki waɗanda za su taimaka su ginaki kuma masu manufa da buri irin na ki.

Share your feedback

Tunanin ku

Yaya ake wankan janaba

March 20, 2022, 8:04 p.m.

Latest Reply

Les go back to islamiyya, Ba'nan Daki Tambaya Ba

Tabbas haka yeke

March 20, 2022, 8:04 p.m.

GASKIYA NAJIDADINLABARIN,NAN KUMANAKARUSOSAI

March 20, 2022, 8:04 p.m.

Hmm Haka Yake

March 20, 2022, 8:01 p.m.

Allah Sarki

March 20, 2022, 7:58 p.m.