Canji da bai kamata ku dame kanku akai ba
Muna girma yanzu. A wannan lokacin akwai canji sosai da zamu masaniya a jikin mu da kuma halayyar mu.
Wadannan canji zasu iya saka mu damuwa, saboda bamu saba dasu ba.
Amma wasun su na al’ada ne kuma bai kamata ku dame kanku ba.
Canji kamar;
Son zama ku kadai
A wannan shekarar mai yiwuwa kuna samun canji a halayyar ku ko kuwa kuna saurin fushi. Shiyasa wasu lokuta muna kule kanmu a daki, ko mu saka sauti mai kara sosai ko kuwa mu toshe kunin mu da na’urar jin sauti ta kunni domin mu guje yin magana da mutane. Mai yiwuwa sinadaran jinsin jikin mu ke sandiyar wadannan halayyar. Wannan ne abun nan dake tasirin halayyar mu da yadda muke ji. Al’ada ce mu so zama mu kadai amma yana da muhimmanci mu guje korin mutane dake kaunar mu. Kada ku ware kanku daga mutanen nan.
Samun yankalin yan maza ko kuwa yin sha’awar su
Muna lokacin balagar mu. A lokacin balaga, shaukin mu zasu kara karfi da tsanani.
Shaukin mu na canzawa da sauri kuma bada sanarwa ba.
Mai yiwuwa mu fara tunanin jima’i. Mai yiwuwa kuma mu fara sha’awar juna.
Dukka wadannan abubuwan al’ada ce.
Abun da mukayi da wannan sha’awar shine abun muhimmanci. Zamu iya yanke shawara mu zama abokai da namijin da muke sha’awa. Yaron dake sha’awar ku zai iya tambayen ku ku fita dashi. Dukkan wadannan abubuwan al’ada ne.
Duk da haka ya kamata muyi tunanin lafiyar mu.
Kada kuyi abokantakar ko soyayyar a boye ko kuwa ba tare da yardar ku ba.
Canji a jiki
Muna girma kuma jikin mu na canzawa.
Idan muna girma zamu lura cewa wasu canji kamar girman nonuwa, ko gashin gaba, ko kuwa jinin al’ada.
Yan maza ma na masaniyar wadannan canjin na jiki kamar girman gemu, katon murya ko kuwa gashin gaba.
Dukka wadannan canjin na al’ada ce. Wasu lokuta wasu abokan mu zasu masaniyar canjin jikin su da wuri ko kuwa suyi girma sa sauri amma ba abun damuwa bane. Jikin mu dabam ne.
Damuwa da kamanin ku
Kuna damuwa da yadda kamanin ku yake? Wannan abun al’ada ce a shekarun ku. Kuna son kuyi kyau. Shiyasa yanzu ana amfani da jan baki, hoda, lalle da sauran su. Har kun fara kula da yadda kuke kwalliya. Kuna son kuna saka kayan yayi. Dukka wadannan abubuwan al’ada ne.
Ba kamanin mu kadai bane ke saka mu kyau.
Samun hali mai kyau, yin taimako, hankali, saka mutane dariya, samun wani kawarewa na musamman ko kuwa kasancewa da hazaka na cikin abubuwa da zasu jawo hankalin mutane zuwa wajan mu kuma ya saka su son mu.
Yin sha’awa akan wasu abubuwa
Kuna ji kamar yanzu kuna sha’awa akan wasu abubuwa kamar jima’i? Abun al’ada ce a shekarun ku. Amma yana da muhimmanci ku samu amsar a wajan kwarai. Wa abubuwa kamar haka zamu baku shawara kuyi magana da wani ko wata amintaccen babban mutum ko kuwa babban yaya.
Wadannan canji ne da kuka lura tun da kuka balaga? Kuyi mana magana akan su a sashin sharhi.
Share your feedback