Mai shawarta: Wani dake bada shawara wa mutane da basu da masaniya
Akwai wani a wani waje da zai iya taimakon ku cin nasarar muradin ku. Wannan mutumin zai iya zama mai shawarta ku.
Wannan mai shawartar zai iya zama wani daya girme ku ko kuwa tsaran ku da zaku iya sama domin shawara.
Idan kuna neman mai shawarta kuna bukatan tuna wasu abubuwa da zaku iya yi da kuma abubuwa da baza ku iya yi ba.
KUYI….
Ku yanke shawara akan irin mai shawarta da kuke bukata
Yakamata Mai shawarta ku ya zama amintacce.
Wani daya samu irin nasarar da kuke so. A ta wannan hanyar, shawarar su zai zo daga wajan masaniya.
Kuyi bincike kusa daku
Mai shawarta ku zai iya zama wani da kuka sani da kuma kuke sha’awa daga nesa.
Zai iya zama wani aboki ko abokiyar iyalin ku, ko wata mallamar makaranta, ko kuwa wata mai kasuwanci a al’ummar ku.
Akwai wata kusa daku dake son wani abu da kuke son ku koya? Kuyi musu magana akan koya daga wajan su.
Ku motsa jiki
Idan mai yiwuwar zama mai shawarta ku wani ne da kuka sani, ku rubuta musu wasika ko kuwa ku samu lambar wayar su, ku kira su, sai ku gabatar da kanku.
Ku gaya musu sune ma’shawarta mafi kyau muku.
Idan kuka tura musu wasika kuma basu amsa ku nan take ba kada ku fid da rai. Ku cigaba da bi.
Kuyi bincike
Ku tambaya akan shirya shiryen shawarta a cibiyar al’ummar ku, ko makarantun ku, ko wajan bautan ku.
Kuyi amfani da kowane lokaci da kyau
Lokacin da kuke kwashewa da mai shawarta ku ya zama mai amfani. Ku kafa ganawa dasu a lokacin da kuka san zasu baku dukkan hankalin su. Ku hadu dasu a kai a kai.
Ku tambaya tambayoyi. Ku rarraba ra’ayin ku dasu.
KADA KUYI…
Taurin kai
Ku kasance a shirye ku amince da shawarar su da kuma sukar su. Ku shirya koyan abubuwa. Kada ku yi kamar kun san komai.
Kuyi amfani da daman nan
Idan mai shawarta ku nada daman taimakon ku, zasu yi. Kada ku dame su suyi. Kuma kada ku tura wasu wajan su ba tare da izinin su ba.
Kada ku bari su ci zarafin ku
Bai kamata mai shawarta ku ya saka ku jin wani iri ba.
Bai kamata su saka ku yin wani abun da baku so ba. Ya kamata kuji tsira idan kuna kusa dasu.
Kada kuji kamar kunyi girma ko kunyi kankani ku nemo taimako daga wajan wani amintaccen mutum da zai iya taimakon ku.
Kuna da mai shawarta? Gaya mana akan mutumin.
Kuna son mai shawarta? Gaya mana irin mutumin da kuke so ya shawarta ku.
Share your feedback