Yadda Amina ta zabi hanyar ta a rayuwa
Kowane karshen mako, naje cibiyar al’ummar da ‘yan uwa na. Muna wasanin allo kuma muyi nishadi soasai. Wani lokaci na lura wasu mutane na zaune a wani daki. Nayi tunanin abun da suke yi, amma ban san yadda zan tambaya ba.
Wata tsakar rana, wata doguwar yarinya ta fita daga wannan dakin. Da sauri na tashi na same ta nace mata sannu. Ta amsa ni da murmushi. Na tambaye ta menene take yi a cikin wajan.
Tace tana halarta wani horaswa na sana’o’i. Tace da ita da sauran mutanen na koyan kwarewa kamar waldi, da dinki, da kuma yin takalmi. Zuciya na ya fara duka da sauri. Tun da dadewa ina da abu ma takalma. Dukka littafai na sun cika da zanen takalma.
A gida, na gaya wa mahaifiya ta ina son na shiga horaswa na sana’o’i. Ta nema bayani daga wajan abokan ta, sai ta yarda.
A lokacin horaswa na sana’o’i, na koya yadda zanyi silifa da takalmin makaranta. Sun koya mana yadda zamu fara kasuwanci da kuma tafiyyad da kudin mu. Bada jimawa ba na yi wa ‘yan uwa na takalmin makaranta. Ana ta masu karamci a makaranta.
A karshen makarantan, akwai wani bikin kammala ajin. Naje saman dakali na karbi takardar shaida na. Mahaifiya ta da yan uwa na nata mun tafi.
A lokaci na gaba, zan koya yadda zan yi rufafen takalma. Kuma zan samu nawa masana’anta; Babban ‘yar uwa ta ma zata hade dani a makarantan horaswar. Ina kafa sana’a daga abun da nake so, kuma rayuwa ta na gaba na kamanin abu mai fiye dana da.
Yan wasan kwaikwayo. Lauya. Masu sakon muhawara.
Akwai sana’o’i masu ban mamaki. Kamar Amina, ba sai kinje wani makarantar boko na kware kafan kiyi abun da kike son yi.
Koda menene sana’ar ki, zaki iya taimaka ki bada gudunmawa domin gyara duniyan. Menene burin sana’ar ki? Gaya mana a shafin sharhin mu.
Share your feedback