Rayuwar wata mai kera manhajar na’urar kwamfuta

Ku kara sanin akan wata yarinya mai rubuta tsarin dokokin kwamfuta

Sannu Yan Springster!

Wata abokiyar mu tazo mana ziyara. Sunan ta Oluwatoyin Yetunde Sanni, kuma tana daya daga cikin masu kera manhajar na’urar kwamfuta. Mai kera manhajar na’urar kwamfuta na kirkira abubuwa dake saka wayoyin mu, da kwamfuta, da kuma sauran na’urori yin aiki a yadda suke yi. Yetunde na aiki da wani kamfanin fasaha da ake kira Andela, wajan da akwai yan mata kamar irin ta (da maza ma) dake yin abubuwa masu kyau game da kwamfuta da kuma fasaha. Kuma tana taimakon sauran mata da yara mata kara koyan abubuwa akan kwamfuta da kuma manjahar na’ura ta wani kungiya da ta kirkira da ake kira Tech in Pink.

Ku cigaba da karanta domin ku kara sanin abubuwa akan Yetunde.

A ina kika tashi?
Nayi girma a jihar Lagos. Daga ungwan Alagbado zuwa Agege, sai Ayobo.

Gaya mana akan farkon lokacin da kika yi amfani da kwamfuta. Kin ji dadin sa?
Na fara amfani da kwamfuta da nake shekaru goma da muke da wani tsohon kwamfutar kan tebur da ake kira- Windows 98 a gidan kaka na. Yawancin lokaci ana amfani dashi domin rubutun makaranta da kuma yin wasanni kamar Mario, Duke 3D da kuma Commando. Kuma eh, naji dadin sa kuma na dan shaku dashi har ya kai iyakan da kaka na take boye linzamin kwamfutar saboda ta rage shakuwar. Kuma na koya yadda ake amfani da allon haruffar da kuma yanken harafi ba tare da taimakon kowa ba.

Yaushe kika yanke shawara cewa kina son ki zama mai kera manhajar na’urar kwamfuta?
Na yanke shawara a shekarar 2013, bayan na kammala karatu na. Da nake bautan kasa (NYSC), ina wani jami’a ina aikin taimakon fasaha sai naga wani wasan kwaikwayon talabijin da ake kira “person of interest”. Akan wani malamin kimiyyan na’uar kwamfuta daya gina wani injin da zai iya yin hasashen ayukkan ta’addanci kafan ya faru. Na iya gano da wasu kalmomi da ake fadi a wasan saboda na karanta darasin kwamfuta da nake makaranta, kuma a lokacin nan ne na san cewa Aritificial Intelligence (wato wata fasaha na’ura kwakwala wacce ke kwaikwayon dabi’un mutane) wata abu ne da zan so na bincika kuma shine ya saka ni fara koyar yadda ake rubuta tsarin dokokin kwamfuta

Wa ya koya miki yadda ake rubuta tsarin dokokin kwamfuta?
Na fara sanda nake makaranta ta darussan da nake yi. Kuma, wata abokiyata ta shirya wani ajin a karshen mako, na koyan yadda ake rubuta tsarin dokokin. Amma lokacin dana dauke shi da zafi shine lokacin dana fara koya da kaina, da takardu da kuma wasu albarkatu da nake samuwa a shafin yanar gizo. Bada jimawa ba bayan nan, na shiga kamfanin Andela.

programmer.jpg

Me kika fi so akan rubuta tsarin dokokin kwamfuta?
Abu daya daga cikin abubuwa da nafi so shine yana barin na gina abubuwa da kaina. Aikin zai iya yin wuya, ko kuwa suyi sauki, kuma akwai masu nishadantarwa. Aikin na bukatan sadaukarwa da kuma daidaici, kuma kuna bukatan kwarin gwiwa. Amma yana da sakayya sosai musamman dadin dake zuwa idan kuka ga abun da kuka kirkira na taimakon rayuwar mutane.

Ya kuke jin da aiki a masana’anta dake cike da maza?
Ban cika son mutane na tambaya na wannan tambayen ba. Wannan saboda koda na san cewa akwai maza fiye da mata. Bana tunanin jinsin halitta na idan aka je wajan yin aiki. Nafi kula da abun da ake bukatan yi da kuma yadda za’a yi sa.
Saboda haka eh, muna bukatan samun bambanci a gaba dayan masana’antu saboda idan akwai bambanci sosai, za’a kara samun kaifin kuzari, amma aiki na na kowane rana daya ne da na kowane namiji da masana’antar.

Wasun mu na so mu zama kamar ki idan muka yi gurma. Ki bamu dabaru.
Kada ku shiga rayuwar fasaha ko kuwa kowane filin aiki domin shine abun yayi. Baza ku iya maida hannun lokaci ba, ku tabbata cewa kuna da dalili mai kyau wa kowane shawara da kuka yanke a rayuwa saboda koda yaushe rayuwa na zuwa a matakai.

Menene abun da kika fi so?
Abun dana fi so shine karfafa mata. Lokaci ya kai da ya kamata iyayen mu su daina mayar da hankali akan yara maza kawai da kuma koya musu yadda zasu inganta aikin su a yayin da zasu koya wa yan mata su zama matan aure masu kyau a duniya. Rayuwar mace dana namiji ya fiye kasancewa matar aure ko mazan aure masu gari.


Gaya mana wani abu da baki taba gaya wa wani ba.

Ina ganin mutane kadan ne a duniya suka san cewa ina son na zama yar leken asiri a wani duniya dabam

Share your feedback