Amma ina da wani abu dabam da zan fadi
Sunana Janet, kuma kwanan nan iyaye na suka koma wani sabon gari. Saboda haka, na bar abokai na a baya, na fara rayuwa a sabon al’umma na.
Bayan da muka dawo nan, ina ta tsoron haduwa da sabobin mutane. Amma sai, na hadu da wannan yaron da ake kira Francis a makaranta.
Ya zo ya same ni a lokacin hutu ya gabatar da kansa. Muka yi labari bayan nan. Ya gaya mun duka abubuwan da nake bukatan sani akan makaranta: Mallamai masu fara’a da kuma wanda ke da tsanani.
Bada jimawa ba, ya zama abun al’ada mu kwashe lokaci tare a lokacin hutu. Kuma wasu lokuta muna tafiya gida tare.
Wata rana, da nake tafiya makaranta a kungiyar abokai na daga ajin mu, daya daga cikin su ta tambaye ni, “toh yaushe zaki gaya mana cewa ke budurwar Francis ce?’
Abun ya bani mamaki! Eh, ina sha’awar sa. Duk da haka, shi ba saurayi na bane. Na tambaya ina ta jin wannan labarin. Tace taji shi yana gaya wa abokan sa a lokacin ajin darasin lissafi.
Abun ya bani haushi sosai na kasa magana a sauran ranar.
Da farko, na yanke shawara bazan kara masa magana ba. Amma sai washegari, na gan sa a wajan cin abinci.
Na lura cewa yana da muhimmanci na fadi abun dake zuciya na. Sai naje na same sa a gaban abokan sa. Na gaya masa labarin dake bazuwa kuma na gaya masa sarai cewa ni ba budurwar sa bane. Har nayi barazana na gaya masa cewa idan bai fadi gaskiya ba, zan daina abokantaka dashi.
Ya gaya wa abokan sa gaskiya, sai suka masa dariya suna tsokanan sa. Har bayan na, ina kan fushi dashi.
Naji kamar yana son ya yanke mun shawara. Kuma abun da bana so kenan. Ina da nawa ra’ayi. Kuma da ya jira, wa ya sani, da muna fita yanzu. Amma bai jira ba, kuma asarar sa ne.
Kun taba samun kanku a irin wannan al’amarin? Ku gaya mana abun da kuka yi a sashin sharhi.
Share your feedback
Tunanin ku
abin abin mamaki ne matuka
March 20, 2022, 7:55 p.m.
Latest Reply
ya kike yssharin
Sannu yarinya! An rubuta wannan makalan saboda ke ne kuma muna farin ciki cewa kina son shi. zaki iya rarraba da abokai ki.