Abun tsoro ne sosai idan kika fara
Farkon al’adan ki zai rikitar da ke kuma ya kunyatar dake. Zai iya baki tsoro ma. Abu ne da aka saba dashi. Abun dadin shine, akwai wata kusa dake data san akan abubuwan nan. Wata da zata amsa duka tambayoyin ki. Mahaifiyarki ko wata babba da kika sanni.
Mun gane cewa zaki ji kunyan maganan irin abubuwan nan. Shiyasa muka sanya wadannan tambayoyi guda biyar da zai taimake ki.
Mama zata iya cewa: alama ne kawai cewa kina girma. kuma ko wanda wata mahaifan ki (yana zama kusa da cikin ki) zai zub da wannan layin dake kama da buhu a cikin mace. wannan layin ne jinin da ke fitowa daga farjin ki a lokacin al’adan ki.
Mama zata iya cewa: Yakamata ki canza audugan al’adan ki ko kayan da kike amfani. Kuma ki riga wanka kullun
Mama zata iya cewa: yakamata ya kai kwanaki uku zuwa biyar, ama wasa mata nayi har zuwa kwanaki bakwa
Mama zata iya cewa: Zaki iya jin kajewar jijiya a cikin ki da kuma kurajen fuska da batan rai da sauran su. Duk wadannan na faruwa ba sabon abu bane.
Mama zata iya cewa: Zaki iya cigaba da abubuwan da kika saba yi ba tare da damuwa ba.
Mun san cewa mai yiwuwa kina da tambayoyi sosai. Wannan hanya ne kawai yarda zaki fara maganan da mahaifiyarki ko wata babba da kika yarda da. Da zaran kika walwala, zaki iya cigaba daga nan.
Kiji yancin tambayan mu tambayoyi akan al’adanki a yankin sharhin mu.
Share your feedback
Tunanin ku
Eh
March 20, 2022, 8:03 p.m.