Dabaru da zasu taimake ku gyara gashin ku
Wasu lokuta busashen yanayi zai iya saka gashi yayi wuya a kula da.
Wannan saboda busashen yanayi na bushar da gashin mu harda fatar gashin. Kuma zai iya rage karfin gashin. Dukka wannan zai iya jawo asarar gashi ko amosanin gashi idan baku kula ba.
Shiyasa muka samo wasu dabaru akan yadda zaku gyara gashin ku a lokacin rani
Ku shafa mai a gashin ku
Kun san yadda fatar jikin ku ko kuwa leben ku ke bushewa, haka gashin ku ma ke bushewa. Busashen yanayi na jawo busashen gashi da fatar gashi. Wannan zai saka gashin yayi karfi kuma ku kasa taje shi. Idan muka taje gahin zai riga karyewa.
Wannan ne yasa muke bukatan shafa mai a gashin mu.
Ku shafa wani abu da zai rage bushewar. Zai iya zama man kade, ko man kwakwa, ko kuwa man zaitun.
Zaku iya hada man kwakwa ko man zaitun a cikin wani kwalba (zaku iya amfani da wani tsohon kwalban tulare, idan kuma baku dashi zaku iya siya). Ku fesa gashin da hadin koda yaushe ko kuwa kowane lokaci da gashin ku ya bushe.
Kuma gashin ku na bukatan ruwa. Ku sha ruwa sosai.
Ku kare gashin ku
A lokacin rani yana da kyau ku kama gashin, ko kuwa ku rufe shi da gyale. Kuma zaku iya yin bacci da gyalen. Wannan zai kare gashin daga bushewa ko yankewa. Kuma idan kuna son ku kare gashin ku, zaku iya kitsa shi.
Ku gwada wadannan dabarun sai ku gaya mana yadda ya muku aiki.
Kuna ganin akwai sauran abubuwa da zaku iya yi domin kula da gashi a lokacin rani? Ku rarrba damu a sashin sharhi.
Share your feedback