Ki dauki matakin yadda ake bi da ke
Mu ne masu mamallakin jikin mu.
Mallakin mu ne tun ranar da aka haife mu.
Wasu mutane na bi da mu kamar jikin mu mallakin su ne.
Ba nasu bane.
Ba mallakin iyayen mu bane, ko na mijin mu, ko na samaran mu, ko na Limamin majami’a, ko na limamin masallaci, ko na mai koyarwar a makarantar.
Ba wanda ke da izinin taba mu a hanyar da bamu so. Ba wanda ke da izinin taba mu idan bamu basu dama ba.
Ba komai idan a gida ne, ko a farfajiyar gidan ku, ko a makaranta, ko a majami’a ko masallaci ko a kan layin unguwar ku.
Zamu iya cewa a’a ba tare da tsoro ko kunya. Ko su waye ne.
Muna da damar kai rahoton kowane da yaki jin mu idan muke gaya musu su daina taba mu.
Baza mu yarda su tsorata mu ba ko su yi barazana domin mu ajiye shi sirri.
Kada ki damu ko mutane baza su yarda da mu ba. Ko mai yiwuwa zasu daura mana laifi.
Ki tuna da wannan. komai muka sanya ko in da muka je, ba wanda yake da daman taba mu idan muka ce a’a.
Babu uzurin ma wani ya taba ki a hanyar da bai dace ba ko ba tare da izinin ki ba.
Jikin ki ne. Kina da yancin sa.
Menene wasu hanyoyi da zaki nuna cewa jikin ki mallakin ne? Gaya mana a sashin sharhin mu.
Share your feedback