Jerin abubuwa da zaku iya yi da kanku: Firem din hotuna

Ku nuna hotunan ku masu kyau

Iyalan mu da kuma abokan mu; muna kaunar su amma kuma baza mu iya ganin su a kowane lokaci ba. Muna dasu a wayoyin mu, a cikin jakunkunan mu da kan taburi.

Wasu lokuta muna son mu nuna hotunan mu a fili da sauran mutane da zusu iya gani. Zai yi kyau mu iya hada firem domin mu nuna wadannan hotunan.

Abun da kuke bukata domin ku hada naku firem na hotuna shine;

  • Kwali (munyi amfani da kwalin taliya)
  • Alkalami
  • Rula
  • Almakashi
  • Reza
  • Alkalamin zane mai launi ( Ba tilas bane)
  • Falen takarda (Ba tilas bane)

Idan kuna da kwali daya zaku iya yin firem guda biyu. Saboda haka idan kuna son kuyi da yawa domin ku siyar wa abokan ku da iyalan ku zaku iya neman kwalaye guda biyar domin ku hada guda goma, kwalaye guda goma kuma zai hada guda ishirin da sauran su.

Mataki na daya
Ku dauke kwalin ku sai ku yanke gefe biyu na kwalin.

f1.jpg

Mataki na biyu
Ku yanke fale falen dake gefen biyu kamar yadda aka nuna a nan kasa.

f2.jpg

Mataki na uku
Ku dauke almakashi sai ku yanke saman kwalin da hankali kamar yadda muka nuna muku a nan kasa. Ku tabbata cewa sauran kwalin bai bace ba. Kuyi wannan wa gefen kwalin biyu.
Ku dauke lokacin ku kuyi wannan domin ku same sa da kyau kamar yadda da muka yi.

f3.jpg f4.jpg F5.jpg F6.jpg

Makaki na hudu
Ku dauke hoton da kuke son ku saka a firem din sai ku saka shi a kan gefen kwalin guda biyu. Ku zana wani layi ya kewaye shi ya nuna wajan da zaku yanke. Sai ku zana wani karamin murabba’i mai dari a cikin wanda kuka zana daga hoton.

F7.jpg

Mataki na biyar
Kuyi amfani da reza ku yanke karamin murabba’i mai darin da kuka zana. Abun da zaku samu kenan bayan kun yanke- Ga misali a nan kasa.

F8.jpg

Mataki na tara
Bayan nan, kuna bukatan abun da zai rike firem dinku. Kuyi amfani da sauran kwalin daya rage ku hada abun da zai rike firem din. Ku zana wani dogon siffa mai gefe biyar kamar na nan kasa sai ku yanke shi daga kwalin.

F11.png F12.jpg

Mataki na goma
Kuyi amfani da gam ku manne abun da zai rike firem din.
Yanzu zaku iya saka hoton ku ta gefen dake bude.
Shikenan kun gama!

F13.jpg

Idan kuna son ku bashi kwaliya, zaku iya yin zane da alkalami mai launi ko kuwa ku hada fure da falen littafi sai ku manna a firem din.

Ku gaya mana irin hotunan da kuke son ku saka a firem dinku.

Share your feedback