Kuduri na na sabon shekara

Muna ta rarraba muradin ta

Sannu Yan Springster! Barka da sabon shekara! Ina farin ciki akan shekarar 2018. Akwai wasu abubuwa da nake so na cimma buri. Na san cewa ba zai zo da sauki ba, saboda haka zanyi aiki sosai. Ga abubuwar dana tsara zanyi:

Zanyi kaunar kaina
A shekarar daya wuce, na guje duba madubi. Bana son hanci na da kuma cinyoyi na. Amma yanzu na san ina da kyau a yadda nake. Don haka wannan lokacin, zan so kai na da kyau. Bazan kara saka kaina jin bakin ciki ba. Idan na sake jin bakin ciki, zan tsaya a gaban madubi. Zan ce, “ Ke na musamman ce kuma babu kamar irin ki”. Zan ta maimaita shi.

Zan yabe wadanda nake kauna
Iyali na da abokai na sun hadu. Ina son su san yadda nake kaunar su. Shiyasa nake basu wasikar godiya. Da kuma kara sauraran su. Ina son na goya musu baya kamar yadda suke goyon baya na.

Siyan karamar waya
Zan siya wayana na farko! Har na kirkira wani dabarar ajiya. Kowane mako, zan raba kudin alijuhu na zuwa biyu. Sai na ajiye daya a gefe, sai kuma na kashe sauran. Zan cigaba har sai na cimma buri na. Na kosa na daina aron wayar mahaifiya ta.

Cin abinci masu kara lafiya
Ina son na kara kula da jiki na. Saboda haka zan rage cin kayan zaki. Daga gasashar garin alkama zuwa chin-chin da kuma biskit, dole dukkan su su tafi. Zan maye gurbin da ‘ya’yan itatuwa da kuma kayan lambu kamar karas, lemu da kuma gwanda. Kuma zan kara shan ruwa. Buri na shine naji dadi kuma na kara kyau a cikin jiki da waje.



Zan koya wani kwarewa
Ina ta son na koya yadda ake gyaran kwamfuta. Ina ta ajiya a watani. Yanzu, kun san mene? Na gama tara kudin! Gobe, Inna na zata taiamke ni rijita a wani makarantar gyaran kwamfuta. Sai na fara koya nan take. Madalla!

Shikenan, yan mata. Allah yasa mu dace a wannan sabon shekarar.

Ku tuna, kuyi kudurin masu sauki. Kada kuyi da yawa a take. A ta nan, zai muku sauki ku cimma burin ku.

Menene kudurin ku na sabon shekara? Gaya mana a nan kasa.

Share your feedback