Yin girma tare, ba da nesa ba

Abokantaka na iya zuwa kusa---ko kuwa nesa---ba tare da bacewa ba

Canji na cikin al’amarin rayuwa. Muna canzawa kusan ko wanda rana. Duk yana cikin abubuwan da ya sanya kika zama mutum. Amma idan abokantakar mu ya canza fa?

Zai iya faruwa idan muna yin girma. Kuma zai iya zamato maras kyau! Zamu iya kwashe lokaci da abokai mu a rana. A rana na gaba kuma, kowa zai koma yin abubuwa daban.

Zainab ta koma wani sabon makaranta. Yetunde ta maida hankali da koyan dinkin ta. Chioma ta koma Lagos da iyayen ta.

Kamar dai kowa ya kama abun gaban sa an share abokantakar. Wannan zai iya sa mu jin fushi ko kishi. Kuma ba komai bane. Yadda muka bi da yadda muke ji ne shine abun muhimmanci.

Abokantaka nada kyau saboda suna nan kamar dankon roba, zai iya ja ba sai ya karye ba. Zamu iya ji kamar mun rabu dasu gaba daya. Amma abun muhimmanci akan abokantaka shine zai iya kara girma kuma. Ba abun dake karewa a dawwami bane!

A maimakon damuwa akan halin da abokantakar yake, zamu iya bincika wasu abubuwan da muke sha’awa. Mu san ko mu waye ne. Duniya babbar waje ne, kuma muna farawa ne. Zamu sha mamakin mutanen da zamu hadu da a hanya. Da kuma sabobin masaniyar da zamu samu.

Zamu iya duba abokan mu dan mu san ko suna lafiya. Kiyi musu magana akan abubuwan da kike yi. Ta hanyar nan ne zamu san ko sun canza ko basu canza ba. Suna gano da kansu ne. Zai kara karfafa abokantakar mu.

Kina kewar was tsofofin abokan ki da suka koma wani jiha ko wanda suke mai da hankali akan wasu abubuwa? Kiyi mana magana a shafin sharhin mu.

Share your feedback