A taimaka, ina bakin ciki da zaman kadaici

Kuma ban san yadda zan inganta rayuwana ba

Kuna jin bakin ciki da zaman kadaici? Ba ku kadai bane.

Al’ada ce aji bakin ciki wasu lokuta. Maii yiwuwa kuna bakin ciki saboda wani abu dake faruwa a rayuwar ku, kamar fadi wani jarabawa ko kewar wani masoyin ku. Ko kuwa kuna damuwa akan canjin jikin ku ko halin da iyalin ku ke ciki.

Ga wasu abubuwan da zaku iya yi domin ku ji dadi….

Tabbataccen Hali
Zai iya yin wuya kuji tabbaci idan kuna bakin ciki. Kuma musamman idan komai dake kewayar ku na tafiya a hanyar da ba daidai ba. Amma dole kuyi iya kokari ku. Zaku iya farawa ta tunatar da kanku akan komai dake baku farin ciki. Abubuwa kamar kasancewa da kaifi, samun iyali na kwarai kusa daku, wani kwarewa da kuke da, ko kuwa yadda kuke da hankali. Wadannan zasu iya saka ku farin ciki.

Ku ajiye wani mujallar
Ajiye wani mujallar na taimako. Ku rubuta abubuwa dake saka ku farin ciki, kamar ruwaito masu kwarin gwiwa akan darajar ku, karfin ku da kuma manufar ku. Ku ajiye shi a wani waje da zaku riga gani.
Ganin sa kullun zai iya saka ku farin ciki. Kuma zai iya tunatar daku ku tsaya da karfi. Idan baku san abun da zaku rubuta akan ku ba, ku same iyayen ku ko masu tsaran ku, ku tambaye su halayar ku masu kyau.

Ku samu wani safga
Ku shiga wani kungiya ko kuwa ku fara wani. Kwashe lokaci da mutane kamar ku nada kyau wa nishadi da kuma aunin darajar ku. Idan kuna son karatu; ku fara wani kungiyar karatu da sauran yara a makarantar ku ko ungwar ku. Kuma zaku iya fara wani kungiyar motsa jiki ko na rawa da abokan ku. Zai janye muke hankali.

Kuyi abun alheri
Ku duba al’ummar ku. Akwai wani kungiya dake bukatar sa kai? Ko kuwa ku gwada ungwar ku. Akwai wani ko wata tsohuwa dake bukatan taimako zuwa kasuwa? Kafan kuyi wani abun alheri, ku tuna cewa tsirar rayuwar ku ya zo farko. Ku samu wani babba da kuka yarda da, kamar iyayen ku ko kuwa malamar ku a makaranta, su taimake ku nemar kungiya mafi kyau ko kuwa mutumin da zaku taimaka wa.

Ku fadi abun dake zuciyar ku
Ance idan muka yi magana akan matsalar mu zamu iya samun taimako. Kuyi magana da wani amintaccen babba akan abun dake zuciyar ku. Yin magana akan yadda kuke ji zai iya kwantar muku da hankali. Idan baku da amintaccen babba a rayuwar ku, zaku iya yin wa wata abokiyar ku, ko kuwa wata mallamar ku.

Da goyon baya na kwarai, abubuwa zasu kasance da kyau.

Kun taba samun kanku a irin wannan al’amarin? Ku gaya mana yadda kuka bi dashi a sashin sharhi

Share your feedback