Jeki yarinya! yadda zaki karfarfa kanki da samun karfin iko

Kina son ki zama yarinya mai karfi? Gwada wadannan siddabaru ki bawa kanki Karin karfi!

Tunanin ku (3)

Kina ji Kaman mara karfi yanzu? Kina ganin babu abun da zaki iya yi ki canza halin da kike ciki? Akwai sannane abu daya da mutane mara karfi ke da shine kalman, “bazan iya ba”

Idan kika ce “baza ki iya ba” yana nufin daya daga cikin abubuwa ukun nan;

  • Bana son nayi
  • Ban iya ba (kina naiman taimako)
  • Ban tsamanin zan iya ba

idan kika fara amfani da “bazan iya ba”, zaki fara ganin asalin matsalan kuma zaki ga yadda zaki samu amsa. Da misali, a maimakon cewa, “ bazan iya yin aikin nan da kaina ba”, Aisha na cewa, “ban san yadda zanyi aikin nan ba, ta san cewa yadda zata gano matsalan shine idan ta tambaya taimako.

kin gani, da zaran kin canza “bazan iya ba” zuwa asalin ma’ana,toh zaki iya yin wani abu akan shi.

  • idan “bana son nayi ne….”, ba damuwa, zai zama zabi zuciyan ki ne
  • idan “ban iya bane….”, toh ki samu yadda zaki koya abun da kanki ko ki tambaya taimako.Babu komai idan kika naima taimako, akwai wasu matsaloli da baza ki iya warware da kanki ba. A wannan irin al’amari, yana da kyau ki sami abokiya da kika yarda da.
  • idan “ban yarda zan iya bane….” toh sai ki tunatad da kanki akan abubuwan da zaki iya yi da kuma fara yarda da kanki.

Ba lalai bane amincewa da kanki ya faru a cikin dare daya ama yana iya faruwa da wani karamin abu. ki daina amfani da kalmomi kaman “ba zan iya ba”. zaki fara jin karfin iko da kuma saka muradi ki ya faru.

Share your feedback

Tunanin ku

Wannan labari yayi dadi

March 20, 2022, 8:03 p.m.

Hakane kuwa, mukasance daya daga cikin masu koyo akoda yaushe.

March 20, 2022, 8:03 p.m.

Allah Ya Saka Da Akhairi

March 20, 2022, 8:03 p.m.