Duniya zata so ta gaya miki ba haka bane, amma kada ki saurara
Koda yaushe ki tuna cewa
Babu kamar irin ki
Babu wani a duniya kamar ke. Ba komai bane idan baki son abubuwan da sauran mutane ke so. Zaki ga ra’ayin ki akan abubuwa dabam ne dana sauran mutane kuma ba komai bane. Ba lalai bane sai kina nan kaman sauran mutane. Babu kamar ki. ke gagarabadau ce. ki kala kanki ko wanda rana a madubi ki fadi wa kanki cewa ke gagarabadau ce.
Kina da izinin zuwa nan
wasu mutane zasu iya sa ki ji kaman haihuwan ki kuskure ne. Wasu zasu ce baki cancanta ki shiga wani kungiya ba. Ki tuna cewa babu kuskure a halitan ki. Wannan ya baki izini ki zo nan kaman sauran mutane.
ki yarda da kanki kuma ki zama mai amincewa kada wani yasa ki ji karancin kanki.
Ba wanda yake mallakinki
Ke ba kujera bane ko kare da mutane zasu mallakin ki da kuma bi dake a munanan yanayi. Ke mutum ce kuma wannan yana nufi cewa rayuwan ki nada muhimmanci. Ki saurara da kuma mutunta na gaba dake. Amma ra’ayin ki ma nada muhimmanci. Ki koya yin magana wa kanki.
Kamani ba komai bane
Kina da buri, kina da kwarewa, kina da zuciyar ki. Akwai abubuwa sosai da kike dashi fiye da fuskan ki da jikin ki. Ya rage miki ki san wadannan abubuwan sai ki fitar dasu dan duniya su gansu. Kyaun ki ya dangata da halayyar ki masu kyau ba akan saka kayan yayi ba kawai. Ki jefar da halayyar ki marasa kyau sai ki kokarin aiki akan halayyar ki masu kyau.
Yar mace abun gagarumi ne
Wasu mutane zasu iya cewa baza ki iya yin wasu abubuwa ba saboda ke ‘yar mace ce. Wasu zasu iya kiran ki jinsin halitta mai rauni. ki tuna cewa kina da hazaka kuma kina da zuciya mai karfi. kada kice wai dan ke mace ce baza ki zama abunda kike so ki zama. ke gabarabadau ce, kina da daraja kuma zaki zama mace mai karfi. Kada kiji tsoron samun zarran yin abu kuma ki gwada yin sabobin abubuwa, wai dan ke mace ce bai zama ki zama mai rauni ba.
Idan kina jin kokwanto akan ki, zaki iya dawowa nan ki kara karanta wannan makalan.
Share your feedback
Tunanin ku
haka ne labarin yayi Kyau
March 20, 2022, 8:04 p.m.