Akan mashawarta
Yana da kyau ku samu wani da zaku iya yin wa magana idan kuna da tambayoyi ko kuwa damuwa. Ko kuwa idan abubuwa suka dan yi wuya. Shiyasa samun Babban Yaya ko yan uwa da zasu iya shawarta ku nada taimako. Kuma idan baku da Babban Yaya, wata mashawarta na iya goyon bayan ku da kuma tafiyad daku.
Idan kuna al’ajabi, mashawarta wani ne da aka yarda da, dake da kwarewa, da zai iya tafiyad daku kuma ya taimake ku cimma burin ku. Zaku iya yin musu magana akan komai. Samari, iyalai, burin ku, da kowane abu.
Mashawarta na sauraran ku. Suna taimakon ku yanke shawara mai kyau da kuma samun dama. Ba sai kun gaya musu komai ba. Amma idan kuka yanke shawara ku gaya musu komai, zasu ji dadin taimakon ku.
Abun mamakin shine, ba matasa bane kadai ke da mashawarta. Harda manya ma nada mashawarta. Ba lallai sai wani sannane ko wani dake da nesa ba. Zai iya zama wani mai hankali da tarbiya dake kusa daku.
Idan kuna son wani ya shawartar daku, kada ku kusanta su haka kawai. A maimako, ku fara da sanin akan su daga wajan wani daya san su soasi. A ta nan, zaku guje rarraba sirrin ku da wani da bai kamata ku yarda da ba. Kuna al’ajabin yadda zaku yi sa? Toh ku karanta wannnan labarin Springster domin ku samu dabaru
Kuna da mashawarta? Idan kuna da, wani buri ne suka taimake ku cimma? Ku rarraba labarin ku da mu a sashin sharhi.
Share your feedback