Jagorar Springster

Dokoki akan yadda zaku zama yan Springster masu kyau

Ya zaku kwatanta yadda kuke son wannan shafin yanar gizo gizo? Mun tabbata cewa kuna son sa sosai.

Muna murna cewa kuna son shafin yanar gizo gizo. Muna son yin muku rubutu.

Mai yiwuwa kuna son shafin yanar gizo gizon saboda yana da nishadantarwa da kuma tsira.

Muna bukatan taimakon ku da cigaba da ajiye shi haka.

Yana daukan hadin kai daga wajan ku domin wannan shafin yanar gizo gizon ya zama wajan nishadi da tsira.

Saboda haka mun hada wani jagora akan yadda muke son yan Springster su nuna halayyar su a shafin yanar gizo gizon.

Muje zuwa:

  • Banda tsangwama. Kada kuyi zagi ko kuwa ku hukunci mutane domin sun tambaya akan wani abu. Kada ku raina mutane a kan shafin yanar gizo gizon. Bu bar mutane su rarraba nasu ra’ayin.
  • Banda rarraba bayanan ku ( kamar lambar waya, ko adireshin gidan ku, ko kuwa adireshin wasikar lantarkin ku, da kuma bayannan shafin sada zumuntar ku). Yana da muhimmanci ku ajiye bayannan asalin shaidar ku a boye idan kuna kan layi, zai tsirata ku. Baza ku san ko mutane na fadin gaskiya ne ko karya idan suna kan layi.
  • Ba’a marabar kalmomin zagi a wannan shafin yanar gizo gizon.
  • Ba’a yarda ayi tallace-tallacen aikace-aikace, shafin yanar gizo gizo, ko kuwa ababanda a wannan shafin yanar gizo gizon.
  • Ku goyo bayan juna kuma ku lura da juna. Akwai wani dake bakin ciki? Ku tura musu sakon rubutu domin suyi farin ciki
  • Koda yaushe ku sanar da Babban yaya idan kuka ga wani na karya doka.
  • Kuyi abokai a shafin yanar gizo gizon amma kuyi hankali dai. Ba kowa bane a kan layi zaku iya walwala da.
  • Koda yaushe Babban yaya zata amsar sharhin ku. Kuyi hakuri. Tana ganin dukka.
  • Ku rarraba makala/ko labarai da abokan ku ko kuwa a shafin sada zumuntar ku. ku ta rarraba!
  • Ku tuna cewa da zaran kuka zama Springsters baza ku canza ba.

Ku kara koyan abubuwa akan tsarin dokokin Springster a wannan makalar

Muna son ku samu masaniya mai tsirata da kuma nishadi a wannan shafin yanar gizo gizon. Hanya daya da zaku iya samu masaniya mai dadi shine idan kuka bi wadannan dokokin.

Akwai abubuwa da yawa da zaku iya koya daga wannan shafin. Ku cigaba da moriyar wannan shafin yanar gizo gizon. Muna kaunar ku.

Share your feedback