Labari na ba gama ba tukuna
Sannu yan mata,
Sunana kahdija, ni daya ne daga yara takwas da mahaifa na suka haihuwa.su na son mu sosai, babana na da aiki mai kyau kuma ya bamu rayuwa mai kyau. Lokaci da ya rasu rayuwar da na lura da ya zu karshe.
A kasarmu, bazawara bata da dama zauna a gidan mijinta. Don haka kawuna ya matsa ma mahifiyata dole mu bar gidan baba na, sai muyi tafiya zuwa karamin makami a kauyen iyalin mamata. don wanna ba fara makaranta da sauri ba. na zauna a gida har wata daya, don in taimakawa ma iyalina muyi tubali don gina sabon gida.rayuwamu ya zama abun ban mamaki .
Amma ka ya na gajiya ko ina jin yanwa, ina kokarin yin aiki makaranta. Na gaya wa kaina na sa kanna waje daya da kuma in mayar da hankali na.kowane lokaci hutu da na samu ina tsakanin aikin gona da tsaftace gidan, ina yin nazarin jarrabawa na karshe don shiga makarantar sakandare .nayi aiki na kwakwalwa lokacin da na wuce kwakwalina na shigarwa tare da alamomi mai kyau.amma bamu iya biyan kudin makaranta ba.na jira har wani shakara don sake jarrabawa a cikin fata cewa zan sami wani makaranta sakandaren na yan mata-kuma na samu.
Wata rana yan makaranta mu sun rinjayi ni zuwa bakin teku da su, a lokacin ne na hadu da wani yaro mai kyau. bayan wannan rana mun fara Magana, da karshe ya tambaye ni in zama budurwa sa.na yadda da shi kuma mu zama ma aurata!ya rinjaye ni in yin jima’I da shi na yarda ,kuma bayan yan watanni na yi ciki.
Ba wanda ya tabba yin mu Magana game da jima’i. ya zo da mutukar damuwa ,ban ma san mai ake kira karewa ba ko yadda za ayi amfani da ita, na lura da shi ya dube ni da kyau, gano cewe na samu ciki ya bani mamaki.mahaifiyata ta yi haushi da ni sosai har da ni ma da kaina.na yi niyya in kare makarantar, amma yin ciki yasa na rasa ci gaba da makarantar
Lokacin da na haifi yaro na, na miji.na cika da ƙauna da farin ciki, wai na kawo rayuwa a cikin duniya. rayuwa har yanzu na da wuya amma mun samu ta. Bayan kusan shekara guda wani mutum ya nuna a gidanmu - ya gaya mu cewa ya na aiki da wani kungiyar ta tallafawa AIDs wadda ke taimakai wa uwaye guda da ba su da miji su koma makaranta don samun ilimi.
Ya gaya mu cewa kafin in cancanci zan yi aiki a matsayin mai horar da yan makaranta kuma zan gaya wa sauran yan mata labarinna don su koya daga gare ni kuma kada su ji tsoron kasancewa da karfi kuma suyi magana idan basu so suyi wani abu. Na yarda! Ina godiya ga damar da zan iya ci gaba da ilimin, da kuma taimaka wa sauran yan mata kamar ni.
Yaro na shekaru shi uku yanzu. Ya kasance mu shekara guda biyu kawai kafin in kammala karatu daga makarantar sakandare. Na kasance ta hanyar da yawa, amma labarinina ba kare ba tukuna. barin makaranta da samun yaro sura ta daya ne kawai a rayuwata. Na san idan na ci gaba da aiki tukuru kuma ba zan daina ba zan iya rinjayar duk wani matsala.
Ko da mutane na iya yin tunani marar kyau game da ni don nayi cika da bayi aure ba, na yi alfaharin kaina don kasancewa misali ga sauran yan mata. Ina tsammanin yana da mahimmanci na ƙarfafa wa yan mata da suke da yara su dawo makaranta, kuma in taimaka ma wasu yan mata su kauce yin ciki.
Kun taba samun kan ku a al’amari irin na khadija Gaya mana yadda kuka shawo kan sa a sashin sharhi.
Share your feedback