Kada ku daina har sai kun kai karshen layi
Sannu yarinya,
Kun tuna na gaya muku a labari na baya cewa zama mai yancin kai na farawa da yin imani da kanku. Idan baku karanta labarin nan ba, ku duba nan
Gaskiyar kenan. Yin imani da kanku shine amsar. Tunda na fara yin tunani masu kyau, abubuwa masu kyau na ta faruwa da ni. Musamman tunda na yanke shawara na fara sana’ar burodi.
Da farko, kamar dai dabara na ba zai yiwuwa ba. Amma gaskiyar shine fara wani kasuwanci bai zuwa da sauki ko kadan.
Akwai abubuwa da yawa da zaku duba. Kuma wannan saboda abubuwa na iya tafi ba daidai ba. A maimako ku tunatar da kanku cewa koda mai ya faru, kuna da karfin zuciya kuma zaku farfado kowane lokaci.
Domin na sa sana’ar burodi na yaci nasara na san cewa dole na magance wasu abubuwa. Mataki na na farko shine na yanke shawara akan inda nake so na siyar da burodi na. Tunda ba zan iya hayan shago ba, nayi tunani na siyar a shagon wani.
Sai na same wata mai siyar da lemun kwalba a kasuwa. Na tambaye ta ko zan iya siyar da burodi na a shagon ta. Nayi mamaki da tace eh. Nayi murna sosai. Na kara jan kusa da zama mai yanci kai.
Sai wani abu ya faru. Da nake hanyar komawa gida daga siyan kayan hada burodin, babur dana hau ya dan samu hatsari. Idannu na biyu ina kallon kayan cafane na suka zube a kasa.
Abun ya bata mun rai! Nayi wa mai shagon alkawari cewa zan kawo mata burodin washe gari. Yanzu bani da kayan hadi ko kudin siyan wani kayan hadi. Ban san abun yi ba. Ina son na fid da rai. Meyasa rayuwa ke kasancewa da wuya?
Da nake tsayiwa a wajan ina kallon muradi na na zama mai yancin kai a kasa, naji muryan kaka na a kai na “ Tunani mara kyau ba zai bada rayuwa mai kyau ba”. Nan take na daina tunani mara kyau sai na fara gaya wa kai na komai zai daidaita. Kafan nan, ba zan fid da rai ba.
Wannan masaniyar ya koya mun cewa tafiyar yancin kai ba hanya mara gargada bane. Za’a samu matsaloli amma abu mafi muhimmancin shine a cigaba da yin aiki sosai.
Kuna son ku san yadda na farfado? Ku duba wannan shafin domin labarin na uku na tafiyana na zama mai yancin kai.
Kun taba samun wani tsaiko a gurin bunkasa wani abu? Ya kuka farfado? Ku gaya mana a sashin sharhi.
Share your feedback