Mutane na canzawa idan jikin mu ya canza
Sanda nake girma, naji abubuwa da yawa game da balaga. Canjin jiki, jinin haila, canjin halayye da kuma sauran abubuwa. Amma ba wanda ya gaya mun akan jan hankali dake zuwa da dukka wannan. Kuna son ku fahimce abun da nake nufi? Ku cigaba da karantawa! * Akwai wani kyakkyawan yaro a ungwan mu da sunan Hassan. Ina sha’awar sa ga shekaru da yawa, amma bai da lokaci na. Nayi kokari nayi masa magana a wasu lokuta, amma baya kula da ni. Na zata baya so na ne. Sai na girmama kai na na share shi. Sai na fara balaga. Nonuwa na da duwawu na suka fara girma. Gaba dayan jikina ya balaga. Duk sanda na kalla madubi, sai na lura da wani canji.
Ashe ba ni kadai bane ke kula da wadannan canjin. Kun san wa ya fara mun magana bayan basar da ni kullum? Hassan! Ya fara da cewa “Sannu”. Sai ya koma da kira na “Babban yarinya”. Sai kuma ya fara ce mun nayi kyau. Har ya so ya saka ni tsallake makaranta domin na kwashe lokaci dashi, amma naki yarda.
Eh, ni “Babban yarinya” ce, amma ina da wayo na. Bazan bari Hassan ya janye mun hankali daga cimma burina ba, musamman saboda na san cewa son da yake mun ba na gaske bane. Na gaya masa ya kyale ni. Kuma yayi. Bai sake matsanta mun ba kuma.
Bani da wanda zan yi wa magana da jiki na ya fara canji. Bana son kanwa ta tayi fama da irin al’amarin nan, shiyasa na gaya mata komai. Yanzu dai ta sani, zata iya daukan shawara mafi kyau idan jikinta ta fara canji. Ina farin cikin rarraba labari na kuma na taimake sauran yan mata.
*
Akwai wanda ya bi daku dabam sanda jikin ku ya fara canzawa? Ku rarraba masaniyar ku da mu a sashin sharhi.
Share your feedback