Uchenna ta raba dabarun ta na sabon shekara
Suna na Uchenna kuma shekaru na goma sha shida. Ina shirya saka shekarar 2018 dina ya zama mafi inganci fiye da wannan shekarar.
Ba laifi shekarar 2017 ya kasance da sauki.
Nayi sabobin abokai a wannan shekarar. Na koya yadda ake yin jakar atamfa.
Mahaifi na ya rasa aikinsa. Rayuwa yayi mana wuya bayan nan. Dan uwa na mai biye dani ya bar makaranta domin ya koya wani sana’a.
Ina son shekarar 2018 ya zama mafi inganci. Ina da dabaru guda biyu wa shekarar 2018.
Na farko shine na fara sana’ar jaka na.
Ina son na nema digiri a jami’a. Ina son na karanta darasin kasuwanci. Wannan darasin zai taimake ni da sana’a na.
Gaskiyar shine bani da kudin dabarun biyu tukunna.
Amma ina tunanin yadda zan tada kudin sana’a na.
Zan tambaye dan uwan mahaifi na Isaac dake kasuwanci ya zuba jari a sana’a na.
Zan tada kudi daga wajan sauran iyalai na kamar yar uwar mahaifiya ta Clara.
Na tsare zan samu kudi na daga siyar da jakunkuna na.
Zan dinka su da keke dinki kaka na.
Na kudurta cewa zan siya fom din jarabawar GCE da kudin dana tara a karshen shekara.
Wata rana na san wannan sana’ar zai kara girma kuma zai bawa ni da iyalai na rayuwa mafi inganci.
Baiyi wuri ku fara tsare abun da zaku yi a shekarar 2018.
Ku rubuta tsare-tsaren ku a wani takarda domin ku tunatar da kanku.
Menene tsare-tsaren ku na shekarar 2018? Kuyi mana magana akan su a wajan sharhi.
Share your feedback