Ya zan gyara shi?
Sannu Babban Yaya,
Shekaru na goma sha bakwai, na saurayi na kuma goma sha takwas. Muna nan tare na shekara daya.
Saurayi na nada hankali kuma yana kula dani. Ya na iya kokarinsa yaga cewa ina farin ciki.
Amma a watani kadan da suka wuce ya koma zama a wani jiha a gaba da Lagos da iyalin sa. Kuma tunda ya koma zama a wajan halayyar sa suka canza.
Bamu magana kamar yadda muka saba. Da kyar yake kira na. Duk sanda na kira sa, yana magana kamar yana saurin ajiye wayan.
Ina son sa sosai kuma yana so na. Bana son nayi asarar soyayyar.
Me zan iya yi?
Da godiya
Amaka.
Sannu Amaka,
Muna godiya da kika yi mana magana.
Soyayya zai iya yin wuya. Yana da kyau ki ga cewa kina kokarin saka shi kasancewa da kyau.
Kin ce bai dade daya koma zama wani waje. Mai yiwuwa yana kewan tsohon ungwan sa ne kuma yana bakin ciki. Mai yiwuwa sabon makarantar sa nada nisa daga gidan sa, kuma tsarin sa ya canza. Mai yiwuwa yana kokarin daidaita da sabon garin sa ne. Gaskiya, hanya daya da zaki iya sanin abun dake faruwa shine idan kika yi masa magana. Yakamata ki samu lokaci kiyi masa magana da kyau.
Ki gaya masa yadda ya canza. Kuma yadda yake saka ki ji. Ki sake tabbatar masa yadda kike kaunar sa. Ki tambaye shi abun da zaki iya yi domin ki taimake shi gyara abun dake saka shi yin wadannan ayukan.
Idan kika yi masa mgana, kiyi hakuri kuma kiyi masa magana da kauna. Ta nan zai san cewa ba fada kike yi dashi ba.
Kada ki damu yarinya!
Ki gaya mun yadda ya kasance.
Babban Yaya.
Share your feedback