Dalilai guda biyar da kike bukatan cin ‘ya’yan itatuwa

Yadda zaki kara wa kanki lafiya

Yau a darasin sanin aikace aikacen gida, mun koya dalilin daya kamata mu ringa cin ya yan itatuwa. Ajin nada sha’awa. Mallamar mu, Mrs Williams tayi mana bayani da kyau. Har ta kawo wasu ‘ya ‘yan itatuwa ta nuna mana. Ta gaya mana mu gaya wa abokan mu abun da ta koya mana. Tunda ku abokai na ne, zan gaya muku komai.

‘Ya ‘yan itatuwa kamar ayaba, lemu da mangoro nada dadi sosai kuma suna da kyau wa jikin mu. Saboda su dabi’ance ne, basu da kowane kimiyya da zai iya jawo mana hatsari. Suna nan cike da sinadarin kara gina jiki, dake taimakon jikin mu kara lafiya da karfi.

Ga abubuwa guda biyar da zamu iya samu daga cin ‘ya’yan itatuwa:

  1. Muna kan girma, saboda haka jikinu na bukatan kuzari sosai. ‘Ya ‘yan itatuwa kamar ayaba, abarba, da kuma gwanda na bada kuzari domin mu samu karfin aikace aikace.
  2. Duk muna son mu samu lafiya. Babu wanda yake son rashin lafiya. ‘Ya’yan itatuwa kamar mangoro, lemu da kuma timatir (E timatir na cikin ‘ya’yanitatuwa) na cike da sinadarin kara gina jiki dake taimakon jikin mu fada da cuta.
  3. Kowa na son fata mai kyau. ‘Ya’yan itatuwa kamar kankana, lemun tsami da kuma lemu na kwashe da sinadarin gina jiki da zai taimaka sa fatar mu laushi da kyali.
  4. Kina son gashin ki ya kara girma da lafiya? Kije wa Avocado, abarba ko gwaiba. Suna da sindarin gina jiki da zai kara miki gashi.
  5. Ya’yan itatuwa kamar lemun tsami, afol, kakamba, avocado dake narkewa da sauri kuma yake samu koshiya da dadewa.

Bayan ajin, nayi wa kai na alkawari cewa zan riga cin ya ‘yan itatuwa kowane rana! Kema kiyi haka. Menene wasu ya yan itatuwa da kike son ci? Gaya mana a shafin sharhin mu.

Share your feedback