Kin shiryawa babban bakon?

Bi da balaga

Balaga lokacin nan ne da jikin mu ke tada sha’awar jima’i. Na yan mata, yana nufin cewa mun isa mu haifa jirirai, amma ba wai mun shirya fara yin jima’i ba.

Na yawwancin ‘yan mata, yana faruwa tsakanin shekaru takwas zuwa goma sha uku. Kada ki damu idan jikin wasu abokan ki ya canza kafan naki ko bayan naki. Yin balaga na zuwa daban daban ma kowane ‘yar mace.

Ga wasu alamar cewa kin fara balaga:

Girman nono
Nono ki na kara girma? Cikakken, katon nonuwa na cikin farkon alamar balaga. Da farko nono daya zai iya girma da sauri yafi dayan. Zaki iya jin laushi da dan jin rashin jin dadi kadan. Wannan ba abun damuwa bane.

Girman gashin gaba da na hammata
Kina da gashi dake girma a karkashin hammatar ki? Kin lura gashin gaba, wannan yana nufin gashin dake girma a wajan farjin ki? Gashin hammattar ki na iya girma bayan gashin gaban ki. Wannan ba komai bane, daidai ne.

Fitar da ruwan farji
Kin lura wani abu kamar madara da launir ruwan kwai a kampai ki? Ana kiran wannan ruwan farji. Jikin ki na hada wadannan sinadarin dake malala dan tsaftace farjin ki. Duk mun gane wannan abun, ba abun da zai kunyatar ki bane. Ki gaya wa wani babba da kika yarda da idan ruwan dake fitowa na da wari. Ko kuwa yana da launin kasa, ko kore, ko kuwa jan launi.

Jinin haila ko kuwa al’ada
Kin fara zub da jini daga farjin ki a kusan kowane wata? Idan haka ne, kin fara al’ada. Yawancin ‘yan mata na fara al’adar su tsakanin shekaru goma sha biyu zuwa goma sha uku. Wasu mata na farawa da sauri, daga shekaru takwas ko kuwa da lati a shekaru goma sha shida. Idan bayan shekaru goma sha shida baki ga al’adar ki ba, kiyi wa wani babba magana akan sa.

Yawan bacin rai
Kina yawan haushi da sauri kwanan nan? Kina jin fushi ba tare da dalili ba wasu lokuta? kina yawan bacin rai da sauri? Duk wannan yana yanki a cikin balaga. Sinadarin kimiyyar nan da ake samar a jiki na canza jikin ki kuma ya shafi yadda kike ji. kada ki damu, ba abun dake damun ki.

Lokacin balaga na iya rikitar dake. Jikin mu na canzawa. Yadda muke ji na canzawa kulun. Zai taimaka idan kika yi magana da wani babba da kika yarda da, kamar mahaifiyar ki, ko yar uwar mahaifiyar ki. Duk, sun ji wadannan abubuwan, sun san yadda kike ji.

Kin lura wani canji kwanan nan? Kiyi mana magana akan sa a shafin sharhin mu.

Share your feedback