Abun da kuke bukatan sani
Sannu Babban Yaya,
Shekaru na goma sha biyar kuma ina da saurayi daya girme ni da shekaru goma sha bakwai. Mun yanke shawara cewa baza mu jira ba kuma. Amma, ina jin tsoron daukan ciki. Da nake karama, mahaifiyata ta gaya mun cewa rungumar namiji kawai zai iya saka ni daukan ciki. Amma saurayi na yace ba zan iya daukan ciki ba a shekaru na. Kina ganin zan iya daukan ciki a shekaru na?
Nagode,
Rikitaciyar kanwa
Sannu Kanwa ta,
Gaskiya idan kika fara jima’i, kuma kin fara al’ada zaki iya daukan ciki.
Babu wanda yake daukan ciki daga runguma.Idan kina son ki kara koya a kan yadda ake daukan ciki, ki duba nan domin ki sani
Amma ba ciki bane kadai ya kamata kiyi la’akari akai.
Idan kina jima’i kina bukatan yin tunanin cutar da ake iya samuwa daga jima’i.
Ana kama cutar jima’i ta yin jima’i da wani dake da cutar.
Za’a iya kama cututtuka kamar kaikayin al’aura, ko kabba da ciwon sanyi, ko kuwa kanjamo idan ba’a yi amfani da kwaroron roba ba a lokacin jima’i.
Yin jima’i babban abu ne. Kuna bukatan yin tunani akan sa da kyau kafan. Zai iya jawo muku rashin lafiya idan sashin jikin ku bai bunkasa sosai ba.
Kuma yana zuwa da abubuwan shauki. Kun shirya wa shakuwar shauki dake zuwa da jima’i?
Sai kuma akwai hatsarin dake zuwa da cuta ko kuwa ciki. Shiyasa kuke bukatan yin tunanin kare kanku (yin amfani da kwaroron roba).
Wannan yana nufin cewa ku nace sai saurayin ku ya amfani da kwaroron roba.
Kuma kuna da ra’ayin ziyarta wani cibiyar lafiya da saurayin ku ko kuwa wani amintaccen babban mutum kamar yar uwar ku, ko innar ku domin suyi wa likitar magana akan zabin kariya.
Amma kun san wadannan zabin basu da tabbas. Kuacewa daga jima’i shine kawai zabi mai tabbas.
A karshe ke kadai ne ke da ikon zabin abu mafi kyau miki idan kika shirya daukan wannan matakin. Amma idan kina yanke shawarar muna son kiyi tunani tsirar ki tukun.
Nagode,
Babban Yaya
Share your feedback