Dabaru da sidabbaru masu sauki
Rayuwa na cike da jinin dadi da kuma bakin ciki. Idan balaga ya fara, bakin cikin na iya fin farin cikin. Kada ku damu. Jikin ku na masaniyar canjin da yawa a lokacin balaga- canjin jiki, shauki, da sauran su. Ba komai bane.
A lokacin balaga, yan mata na fara girmar da nono kuma suna fara jinin haila. Muryar samari kuma na kara zurfi. Wa yan mata da samari, gashi na fara girma a hammatar su da kuma gaban su. Da dukkan wadannan sabobin sinadaran jinsin dake cikin jikin ku, mai yiuwa ku samu canji a halayar ku kuma ku samu kurajen fuska.
Mun san cewa kurajen fuska na iya zuwa da zafi.
Duke da haka, labari mafi kyau shine basu zama har abada. Baku yarda ba? Ku gwada wadannan magungunan na halitta:
Ku sha ruwa sosai
Shan ruwa sosai nada da kyau wa jiki. Gaskiyar shine yana kara inganta kayan dake nakar da abinci a cikin jiki, yana cire datti, kuma ya cika jikin ku da sinadaran gina jiki. Sakamakon? Fata mai kyau mai walkiya da lafiya, yarinya.
Gaurayan da za’a iya yi a gida
Ku markade ayaba. Ku diba cokalin zumu guda biyu biyu sai ku hada komai tare yayi laushi. Da hankali ku baza shi a kan fuskan ku da wuyan ku. Ku bari ya bushe na minti goma zuwa ishirin, sai ku wanke fuskan ku. Kuyi sa so biyu a mako.
Ku ya da gajiya
Kuje da hankali. Ku samu isasshen bacci da motsa jiki na kwarai. Duka wannan zai taimake ku kwantar da hankalin ku. Idan kuka rage gajiya, jikin ku zai kara ingantawa.
Toh shikenan yan mata. Kun san wasu dabaru da sidabbarun yin watsi da kurajen fuska? Ku gaya mana a nan kasa.
Share your feedback
Tunanin ku
Danbaiwa
March 20, 2022, 7:54 p.m.