Ki koya yadda zaki tsaftace farjin ki
Ki koya yadda zaki tsaftace farjin ki
Yan mata sunfi saurin kama cuta fiye da maza. Yanayin yadda jikin mu yake ne.
Shi yasa yake da kyau mu sa ido a abubuwan dake faruwa. Musamman a wajan farjin mu. Yana da muhimmanci ki san abubuwa na al’ada. Kuma da wanda ba na al’ada ba.
Nan kasa ga wasu abubuwa masu muhimmanci daya kamata ki sami.
Fid da datti daga farji
Wannan dattin dake da launin mai ruwan kwai ko kamar madara da muke gani wasu lokuta a kampai mu shine abun da ake kira dattin dake fitowa daga farji.
Ba komai bane. Yana taimakon tsaftace farjin ne kawai.
Amma dai kada launi datti dake fitowa ya zama mai launin kasa ko kore.
Idan naki nayi haka, dan Allah ki kai rahoto a wajan wani babba da kika yarda da ko wajan wani ma’aikatan asibiti.
Kaikayi da zafi
Farjin ki na miki kaikayi? Farjin ki na miki zafi?
Kina jin zafi idan kina fitsari?
Wannan ba na al’ada bane. Mai yiwuwa alamar kamuwa da cuta ne.
Kina bukatan taimakon asibiti. kiyi wa wani babba magana tun yanzu.
Warin farji mara dadi
E farjin mu nada nasa warin. Wannan al’ada ce. Amma kada warin yayi mara dadi.
Idan kika ji wani wari mai karfi mara dadi, lokaci ya kai ki duba abubuwa. Kiyi magana da wani babba da kika yarda da.
Kina tunanin yadda zaki tsaftace wajan? Ga wasu siddabaru:
Kina da tambayoyi akan lafiyan jikin ki? kiyi magana da wani babba da kika yarda da ko kuwa ki gaya mana damuwan ki a shafin sharhin mu.
Share your feedback