Ku karanta wannan kafan kuyi jima’i

Chidinma ta gaya mana komai

Tunanin ku (5)

Nayi jima’i na farko da nake shekaru goma sha biyar.

Saurayi na na zama a karshen layin unguwan mu. Mun hadu a bikin karshen shekara na unguwan mu. Bayan da muka fita na watani uku, ya tambaye ni nayi jima’i dashi. Na san cewa ban shirya ba, amma ina son na kwantar masa da hankali. Ina son na nuna masa cewa ni “Idannu na sun bude”. Sai na yarda muka yi jima’i.

Bayan nan, ya fara guje ni. Dana tambaye sa ko zamu iya haduwa, ya kawo uzuri iri iri. Ya daina amsa sakonni na, da wayoyi na. Abokiyata tace yayi “ harkan bacewa”. “Harkan bacewa” na nufin wani ya yanke hulda da mutum ba tare da bayani ba. Na kasa yarda. Naji kamar yayi amfani dani ne.

Nayi kokari na tuna da dalilin daya sa na kwana dashi. Nayi tunanin yadda ya saka ni ji bayan dana yi. Naji kamar bani da ikon jiki na kuma. Nayi bakin ciki. Ina bukatan yin wa wani babba magana kafan abubuwa su kara muni.

Wata rana, nayi wa yar uawata magana. Na gaya mata komai. Abun da wuya, amma na yarda da ita sosai. Na san cewa zata ajiye mun sirri na.

Ta taimake ni ganewa cewa yin jima’i a shekarun kuruciya na zuwa da kasada. Yana jawo shauki da yawa: tsoro, jin laifi, da na sani, fushi da kuma fargaba. Ta tabbatar mun cewa shauki na ba komai bane, saboda haka kada na dame kaina.

Nan gaba, dole na gafarta wa kai na. Eh, na san cewa kuna ji kamar yayi tsanani. Amma ya biya sosai. Na amince cewa ban yi abu da ba daidai ba, kuma ba laifi na bane.

Idan zan iya maimaitawa, zan tabbata cewa ina nan a shirye. Na farko, dole saurayi na dani muyi magana sosai mu amince da juna. Ba zan iya yinnabun da zai hana ni sakewa ba. Abu mafi muhammanci, ba zan yi domin na gamsar da wani ba.

Jima’i. Kalma daya, tambayoyi dubu. Lokacin daya dace a yi, da lokacin da bai dace ba. Abun shine, babu amsa mai sauki. Duk da haka, idan kuka zabi kuyi jima’i, akwai abubuwa daya kamata ku sani. Munji dadi da Chidinma ta raba labarin ta da mu.

Kun koya wani abu daga masaniyar Chidinma na farko? Muyi magana a sashin sharhi.

Share your feedback

Tunanin ku

Tabdin gsky ne

March 20, 2022, 7:54 p.m.

Latest Reply

Sannu yarinya! An rubuta wannan makalan saboda ke ne kuma muna farin ciki cewa kina son shi. zaki iya rarraba da abokai ki.

Sosaima kuwa, jima'i hanya ce mai kuma mai cutar da jama'a ldan basuyi aure ba

March 20, 2022, 7:54 p.m.

hmmmn

March 20, 2022, 7:53 p.m.

gaskiya shaawa tana sanya yin jimai ko baashiryaba

March 20, 2022, 7:53 p.m.