Bari mu fadi gaskiya
Jima’i. Kowa ya san komai a kan sa.
Amma sun sani da gaske?
Akwai karya da yawa da kuma jita-jita akan jima’i. Kuma basu taimakon mu. Saboda haka, yakamata mu raba gaskiya daga karya yanzun nan. Yana da muhimmanci mu san yadda
jikin mu da hankalin mu ke aiki. Muje zuwa:
Karya daya
Baza mu iya daukan ciki ba a ranar da muka fara jima’i. Idan muna al’ada, ko kuwa idan muka yi jima’i a wasu irin hanya, ga misali, a tsaye.
Gaskiya daya
Domin daukan ciki ya auku, dole a hada maniyyin namiji da kuma kwan mace. Baya danganta da lokaci ko ranar da aka yi jima’i, ko kuwa irin hanya da muke yin jima’i. Koda munyi wanka, ko gudu a cikin daki, ko kuwa yin fitsari bayan jima’i, ba zai hana daukan ciki ba. Muddin dai baku amfani da kwaroron roba ba, akwai damar daukan ciki.
Karya na biyu
Yin jima’i da budurwa zai iya warkar da namiji mai cutar da ake samuwa ta jima’i (STI).
Gaskiya na biyu
Idan kuna da cutar da ake kamawa ta jima’i, zai fi kuje asibiti domin gwaji na kwarai da kuma magani. Yin jima’i baya warkar da kowane cuta. Mutane dake fadin wadannan abubuwan na son su jawo matsala ne. Kada ku damu da su.
Karya na uku
Yan mata dake yin jima’i da kuma ke yin tunanin jima’i basu da da’a.
Gaskiya na uku
Yin sha’awa akan jima’i da kuma yin jima’i al’ada ne da mutane – Yan mata, maza da kuma kowa. Ku tuna cewa, yan maza basu fi yan mata ba. Kamar su, muna da tambayoyi da kuma ra’ayi akan jima’i. Baya nufin cewa mu yan mata mara da’a ne. Yana nufin cewa mu mutane ne kawai. Bai kamata a kunyata mu ba.
Karya na hudu
Idan namiji na son mace, dole ta kwana da shi koda tana son tayi ko bata son tayi.
Gaskiya na hudu
Jikin mu mallakar mu ne. Jikin mu ba wani kyauta bane da wani ya bamu haka kawai. Bamu rike wa wani bashin jima’i ba, koda ya muke kaunar su. Yin jima’i ra’ayi ne da zamu iya yi da kanmu idan muka shirya.
Karya na biyar
Idan baku son kuyi jima’i da wani namiji, zai iya tilasta ku canza ra’ayin ku.
Gaskiya na biyar
Muna ganin wannan koda yause a takardu da kuma wasannin kwaikwayo. Wata yarinya taki fita da wani yaro da bata sha’awa, sai ya matsa mata har sai ta yarda. Wannan na cusa ra’ayi a rayuwa na asali cewa, idan muka ce a’a, muna nufin eh. Amma gaskiya, “a’a na nufin a’a” kuma “eh na nufin eh”. Kada kowa ya zalunci mu yin abun da bamu son muyi. Idan bamu son muyi jima’i da wani, mu tsaya da gaske mu ki. Koda a wani lokaci mun yarda, muna da yancin canza ra’ayin mu.
Ku lura cewa: Kauce jima’i shine hanya mafi kyau da zaku guje daukan ciki ko kuwa kama wani cutar jima’i (STI). Ku duba nan domin ku koya akan jima’i na tsira. Kuna da wani damuwa?. Kuyi magana da wata ko wani amintaccen babban mutum ko kuwa wata/wani likita.
Share your feedback